Dan Thailand zai sha dauri kan zagin Sarki

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Akwai doka mai tsauri a kan masarautar Thailand

Kotun soji a kasar Thailand ta yanke wa wani mutumi daurin shekaru 30 a gidan yari saboda wallafa hoto na batanci ga masarautar kasar.

Wannan hukuncin shi ne mafi tsauri da aka yanke wa wani mutum kan irin wannan laifin.

Mutumin mai suna Pongsak Sriboonpeng ya amsa laifin rubuta sakonnin batanci.

Masu aiko da labarai sun ce masu shigar da kara na gwamnati sun kara yawan shigar da kara tun lokacin sojoji suka kifar da gwamnatin farar hula a bara.

A ranar Alhamis ne aka yanke wa wani mutumi mai tabin hankali hukuncin daurin shekaru biyar saboda lalata hoton Sarkin kasar.