'Yan takarar Republican sun yi muhawara

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan takarar shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar Republican

Mutane goma wadanda suke sahun gaba wajen neman takarar shugabancin Amurka a karkashin jam'iyyar Republican, sun gabatar da muhawara ta farko a shirye-shiryen zaben shugaban kasar da za a yi a shekarar 2016.

Muhawarar -- wadda aka nuna a gidajen talbijin har na tsawon sa'oi biyu, ta bai wa al'ummar Amurka damar tantancewa tsakanin 'yan takarar.

Dukkanin 'yan takarar sun yi tarayya wajen sukar lamirin 'yar takarar jam'iyyar Democrat, Hillary Clinton.

A watan Nuwambar 2016 ne za a yi zaben shugaban kasa a Amurka a lokacin da wa'adin shugaba Obama na tsawon shekaru takwas zai kare.