Yaje-yajen aiki za su kassara Ghana

Likitoci sun kaurace wa asibitin Ghana
Image caption Likitoci sun kaurace wa Asibitoci a Ghana

Masu lura da al'amura a kasar Ghana suna ci gaba da tofa albakacin bakinsu dangane da yanda bangarorin ma'aikatan kasar ke shiga yajin aiki, wanda suka ce ka iya durkusar da kasar.

A halin da ake ciki dai Malaman Jami'a da manyan makarantun kasar sun fara yajin aiki, yayin da Likitoci suka shafe sama da makwanni biyu suna nasu yajin, duka da nufin matsa wa gwamnati lamba domin ta biya su wasu hakkokinsu.

Rahotanni daga kasar na cewa yajin aikin Likitocin ya jefa al'umar kasar, musamman majinyata cikin wani mawuyacin hali saboda karancin Likitocin da za su duba su.

Alhaji Alhassan Abdullahi, mai sharhi ne a kan al'mauran yau da kullum a Ghana, kuma a tattaunawar da ya yi da BBC ya ce ya kamata gwamnatin kasar ta gaggauta duba hanyoyin daidaitawa da ma'aikata, idan ba haka ba lamarin zai baci.