An yi wa kamfanin Carphone kutse

Carphone Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wayar salular kamfanin Carphone Warehouse

Wani kamfanin sayar da wayar salula na Biritaniya, Carphone Warehouse, ya ce masu kutsen kwamfuta sun sami nasarar kaiwa ga bayanan masu hulda da kamfanin su kusan miliyan biyu da rabi.

Ranar Laraba ne kamfani ya gano cewa an keta tsaron nasa, amma sai yanzu ne ake samun cikakken bayani.

Kamfanin na Carphone Warehouse ya ce watakila bayanan da aka samu har na katin banki da aka sirranta, na kusan mutane dubu casa'in.

Kamfanin ya ce a halin yanzu ya tanadi karin tsaro a kamfutocin nasa.

Kamfanin ya kuma ba masu amfani da wayar salular sa hakuri dangane da abin daya abku.

Kazalika, kamfanin ya ba da shawarar yadda masu amfani da wayoyin salular sa zasu takaita hadarin dake tattare da satar bayanan sirrin su sakamakon wannan kutsen daya janyo keta tsaron abokan huldar kamfanin na Carphone.