Goyon bayan yarjejeniyar nukiliya da Iran

Dakarun sojin kasar Iran Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dakarun sojin kasar Iran

Kwamandan rundunar sojin kasar Iran Hassan Firouzabadi, ya nuna goyon bayan sa ga yarjejeniyar makamashin nukiliya da Iran din ta cimma da manyan kasashen duniya.

Kafafen yada labarai na kasar sun ambato kwamandan rundunar sojin wanda na hannun daman shugaban addinin kasar Iran din ne, na zayyana irin gajiyar da Iran za ta samu wadanda ya ce masu adawa da yarjejeniyar suka kauda kai akai.

Akwai wasu da dama a Iran da Amurka da ke ta sukar yarjejeniyar.

Sai dai rahotanni sun ce nuna goyon bayan da Janaral Firouzabadi ya yi zai taimaka wajen sauya tunanin masu sukar lamarin.