Wayar HTC na adana hoton zanen yatsu

Wayar HTC Hakkin mallakar hoto HTC
Image caption Wayar HTC na adana hoton zanen yatsu

Masu bincike kan sha'anin tsaro sun gano wasu hanyoyin da za'a iya tantance bayanan zanen dan yatsa a wayar salula ta HTC.

Wasu kwararru hudu daga kamfanin FireEye dake samar da tsaro sun gano bayanan dan yatsa a wani rumbun adana hotona da bai da wahalar tantancewa.

Su dai wadannan masu bincike su ne; Yulong Zhang da Zhaofeng Chen da Hui Xue da kuma Tao Wei - kuma sun gabatar da sakamakon binciken nasu ne wani taro da aka gudanar a Las Vegas.

Da dama daga cikin masu amfani da wayar salula ta komai da ruwanka na amfani da dan yatsar su wajen rufewa da bude wayoyin su, ko kuma su bada umurnin cikini ta hanyar sadarwa ta Internet.

Amfani da bayanan dan yatsa ko kuma hoton fuska wata hanya ce da ke ba jama'a damar sarrafa wayoyin a saukake, sai dai wasu kwararru na ci gaba da tababa game da karkon amfani da wannan hanya.