Nigeria za ta fara amfani da asusun bai daya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaba Buhari ya bayar da umarnin amfani da asusun bai daya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bai wa ma'aikatun gwamnatin tarayya da hukumomin kasar umarnin su soma biyan kudaden shigarsu cikin wani baitulmali na bai-daya.

Wata sanarwa da ta fito daga fadar mataimakin Shugaban Najeriya ta ce wannan mataki ne da aka tsara shi musamman domin tabbatar da gaskiya da adalci wajen yadda ake kashe kudaden gwamnati, kuma wannan umarni zai soma aiki ne nan take.

Malam Garba Shehu, mai magana da yawun Shugaban Najeriya, ya ce a bisa tsarin dokar kasa, gwamnatin tarayya da ta jihohi da kuma ta kananan hukumomi asusu daya za su dinga amfani da shi.

Ya kara da cewa idan har gwamnatin jiha da ta kananan hukumomi ba su san me yake shiga asusun gwamnatin tarayya ba, to anan ne gwamnatin tarayya ke yin duk irin badakalar da take so da kudin gwamnati.