An kama masu cin zarafin yara a Pakistan

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana cin zarafin yara a Pakistan

An kama wasu mutane bakwai da ake zargin su da hannu a badakalar lalata da cin zarafin kananan yara a gabashin Pakistan.

Ministan lardin Punjab Shahbaz Sharif, ya bayar da umurnin a gudanar da cikakken bincike a kan rahotanni da ke cewa ana cin zarafin daruruwan kananan yara.

Wasu kafafen yada labarai na cikin gida sun ce akwai gungun mutane da ke shirya faya-fayen bidiyo na batsa, inda suke nuna yadda ake cin zarafin kananan yara maza, daga bisani kuma a karbi kudade daga iyayen yaran bayan an yi barazanar yi musu sharri.

Wannan badakalar dai ta yi kamari ne a wani kauyen da ke kusa da garin Kasur.