An kusa sakin Limaman da aka sace a Tanzania

Image caption Shugaban Tanzania Jakaya Kikwete

Mutumin da yake sasantawa domin sakin malaman Islama bakwai da aka sace a Tanzania a makon da ya gabata ya shaida wa BBC cewa an kusa a cimma yarjejeniya.

Sheikh Sulaiman Mohammed ya ce, tawagar masu sulhun suna ganawa da wadanda suka sace Malaman sun kuma ce ba a gallaza musu.

A hirar da ya yi da sashen Swahili na BBC, Sheikh Sulaiman ya ce "Sun nemi a basu kudi sun kuma yi barazanar ci gaba da boye malaman idan har ba a basu kudin ba."

Ya kara da cewa masu satar ba malaman suka yi niyyar sace wa ba, sun dai kasance a wajen ne kawai lokacin da al'amarin ya faru.

A makon da ya gabata ne aka sace wadannan malamai a kasar Tanzania da ke gabashin Afrika.