An kaddamar da hare-hare a Turkiya

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption 'Yan tayar da kayar baya sun zafafa hari a Turkiya

An kaddamar da hare-hare kan jami'an tsaro a yankuna daban-daban na kasar Turkiya.

A lardin Kurdawa na Sirnak da ke kudu maso gabashin kasar, an kashe 'yan sanda hudu a lokacin da aka dasa bam a gefen titi.

Sannan kuma aka hallaka soja guda lokacin da aka kai hari a kan jirgi mai saukar ungulu.

A birnin Istanbul kuwa, an hallaka dan sanda daya lokacin da dan kunar bakin wake ya kai hari a wani caji ofis.

Sannan kuma an kai hari a karamin ofishin jakadancin Amurka.

A halin yanzu dai Turkiya na cikin shirin kota-kwana, tun bayan da ta soma kai hari a kan mayakan IS a Syria da kuma tsagerun Kurdawa a kudancin Iraki a watan da ya wuce.