Asibitin Abuja ya nuna yadda ake tiyata

Hakkin mallakar hoto Abuja National Hospital
Image caption Asibitin Abuja ya kafa tarihi a Nigeria

Babban asibitin Nigeria a Abuja ya yi bayani daki-daki a shafin Twitter a kan fidar da aka yi domin gyara wani rami a zuciyar wata yarinya 'yar shekaru takwas.

Asibitin kasa na Abuja shi ne na farko a Najeriya da ya bayyana aikin fida daki-daki yayin da aikin ke gudana, a shafinsa Twitter.

Kakakin asibitin, Dokta Tayo Haastrup, ya ce an yi hakan ne domin nunawa duniya kwarewar 'yan Najeriya.

A baya dai asibitoci a kasashe kamar Canada sun bayyana aikin fida a zuciya daki-daki a shafin Twitter.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Hakkin mallakar hoto BBC World Service