Ba ma iko da sararin samaniyar Najeriya - Ghana

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba John Mahama na Ghana

Hukumar kula da zirga-zirgar jirage ta Ghana, ta musanta rahotanni da ke cewar kasarta tana iko da sararin samaniyar Najeriya da ke gabar tekun Guinea.

Wannan na zuwa ne bayan da a baya-bayan nan shugaba Buhari ya bai wa hukumar kula da zirg-zirgar jiragen sama ta Najeriya umarnin karbe ikon sararin samaniyar kasar na gabar tekun Guinea daga Ghana.

Sai dai a cewar Ghana tana kula ne kawai da sararin samaniyar kasar Togo da kuma Benin.

Mataimakin Darakta Janar na hukumar kula da jiragen sama na Ghana, ya ce hukumar da ke kula da zirga-zirgar jiragen sama na duniya ta tura tawaga Najeriya domin tabbatar da furucin shugaba Buhari a kan umarnin da ya bai wa ma'aikatar kula da sifirin jiragen sama ta kasar.