Babu tawagar gwamnatin Nigeria a hajjin bana

Hajji
Image caption Gwamnatin Nigeri na raba kujerar hajj kowanne shekara a mtasyin tawaga ta musamman

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya ce gwamnatin kasar ba za ta aika da tawagar gwamnatin tarayya ta musamman ba Hajjin bana.

Sai dai shugaban kasar ya ce gwamnatocin jihohi na da iko su tura tare da kuma daukar dawainiyyar tawagar jami'an gwamnatin jihohi idan suna bukata.

A hirar da BBC ta yi da Garba Shehu mai ba shugaban kasa shawara a harkar yada labarai yace, wannan mataki na wannan shekara ne kawai, kuma gwammnati za ta aika da ma'aikatan kula da lafiya da sauransu domin taimakawa alhazai kamar yadda aka saba.