Adobe zai fara biyan mata kudin hutun shayar da jariri

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kamfanin Adobe ya yarda ya biya mata masu shayarwa na dogon lokaci

Kamfanin Adobe yana wani yunkuri na inganta aikin mata masu shayarwa har na tsawon kimanin takwas.

Kamfanin dai ya amince da ya fara biyan mata masu aiki a Adobe wadanda suka haihu.

A yanzu haka za a rinka biyan duk wata mace ma'aikaciyar kamfanin wadda ta haihu, kudin hutu har na kwanaki 26.

Akwai kuma karin alawus na rashin lafiyar ma'aikata da iyalansu.

Adobe kamfani ne mai samar da dabaru na zamani a harkar fasaha.

kwararru dai na ganin cewa wannan mataki da kamfanin ya dauka zai taimaka gaya wajen ba wa mata karfin gwiwar aiki a masana'antar.

Kamfanonin NetFlix da na Microsoft su ma sun fara biyan kudaden hutun haihuwa ga iyaye mata da ma mazajensu, har na tsawon shekara guda.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A baya dai kamfanin ba ya biyan kudi idan har kwanakin da aka deba wa matan ya wuce

A baya dai idan mace ma'aikaciya ta haihu to za a rinka biyan ta ne iya kwanakin hutun da aka deba ma ta wanda kuma aka yi yakinin cewa bai taka kara ya karya ba.