Me ye kwalliya ta al'adar Afrika ke nufi a wajenka?

Ma'aikatan BBC sun kure adaka domin bayyana yadda kwalliya irin ta al'adun Afrika ta ke nufi a gare su.

Sun bayar da hujjoji ga manufar kwalliyar al'adun Afrika a garesu.

1- Kim daga Zimbabwe, Sashen BBC na Focus on Africa.

Hakkin mallakar hoto

"Kwalliya ce da ta wuci atamfa kadai. Samun basirar zaban abin da ya dace da kai da kanka. Masana'antun suturun Afrika na bunkasa, kuma an fara wuce kwalliya irin ta atamfa kawai."

2- Prudent daga Rwanda, Ma'aikaci a BBC Great Lakes.

Hakkin mallakar hoto

"Ni bani da wata masaniya a harkar kwalliyar Afrika. Ina saka sutura ne kawai. Ina saka jins, amma a gani na, ni dan gargajiya ne domin ina saka suturun gargajiya."

3- Florentine daga Burundi, Sashen BBC na Great Lakes.

Hakkin mallakar hoto

"Afrika tana da kwalliya ta asali wacce ake dinkawa da hannu. Al'adar Afrika ne koyar sana'ar hannu domin a dogara da kai. Ana kera kayan kawa masu armashi wadanda kwalliyar su bata satuwa"

4- Bilkisu Babangida, daga NigeriaSashen Hausa na BBC.

Hakkin mallakar hoto

"Kyau na asali da al'adun Afrika. Duk inda ka je a duniya, zaka tarar cewa 'yan Afrika sun fita daban da sauran mutane, inda kana ganin su ka san suna alfahari da al'adar su."

Tsarin tufafi: An hada kwalliyar sakar Afrika da ta larabawa. An hada kwalliyar tasu ne, kuma hakan shi ne kwalliyar Afrika ta zamani. An hada sakar ne da kaya masu santsi da kuma kwalliyar dinkin zare.

5- Aichatou Moussa, daga Niger,Sashen Hausa na BBC.

Hakkin mallakar hoto

"Ina son sa suturar Afrika saboda an fi samun sakewa cikin su. Kalolin su kuma suna sanya ni cikin farin ciki a koda yaushe."

6- Ahmed Abba Abdullahi,Sashen Hausa na BBC

Hakkin mallakar hoto

"Ya tanadi komai-da-komai. Duk inda na je, ina son sa kayan gargajiya, saboda shi ne tushe na."

7- Ibrahim Shehu Adamu,Sashen BBC Focus on Africa.

Hakkin mallakar hoto

"Kwalliya irin ta al'adar Afrika wani tsari ne da ke nuno al'adun Afrika da kuma halayyar mutanen Afrika, wanda ya ke nunawa duniya al'adun mu na gado. Ni a gani na kwalliyar Afrika ta na nuna halayyar mutum a tufafin sa da kuma fitowa da yadda ake alfahari da al'adar sa."

8- Rachael daga UgandaEditan shafin BBC na Focus on Africa.

Hakkin mallakar hoto

"Kwalliyar tana nuna asalina. Ba koda yaushe nake sa suturun Afrika ba sai lokuta na musamman. Ina alfahari da kwalliya irin ta al'adar Afrika musamman in na je London inda nake fita daban da sauran mutane da ke sanye da kayan nasara."

Rachael ta saka suturar gargajiyar kasar Uganda, wanda ake cewa 'gomesi' ko kuwa 'busuti'.

9- Veronique, daga Kamaru,Sashen BBC Focus on Africa .

Hakkin mallakar hoto

"Kwalliyar Africa tana martaba mutum"

10- Mohanad Hashim, from Sudan,Sashen BBC na Focus on Africa.

"Suturu masu kala daban daban da fadi da kuma kwalliya ta daban. Kwalliyar da ke da dan almubazaranci a tare da ita, musamman ga mata, a kuma samu kaloli masu daukan ido."

Tsarin sutura- Kwalliyar asali ta hamada

Matasa sun fara canza tsarin suturun gargajiya, amma asali fararen kaya ake sakawa.

Sakakkun jallabiya ake sawa saboda zafi, an kuma dinka su hakan ne domin ka iya fifita lokacin zafi.

Hakkin mallakar hoto

Ana sanya tufafin wanda ake ce wa 'Jinaah Umm Jaku' watau gaba zuwa baya ko kuma baya zuwa gaba.

Hakan ya sa a rana ake iya juya shi gaba a baya idan ya yi dau'da.

Akwai 'yar ciki kuma, wadda ake sakawa a cikin gida watau 'Aa'ragi'.

Ana iya lulluba da rawani lokacin kwanciya da yake yawan yadin yana kaiwa kimanin tsawon mita 2.5 zuwa 3, ana yafawa saboda ana yin yadin ne isasshe.

Akwai 'Malfaha' ko kuma 'Shal', wanda shi ma karin yadi ne da ake rufe fuska da shi.

11- Hélène, daga Faransa,Sashen BBC Afrique

"Kana iya zaban wanda zai maka dinki, ka kuma tsara yadda za'a yanka tufafin, amma kana da hurumi wajen zabin irin suturar ka. Ba sai mun je shagon tela ba, akwai tsare-tsare da kaloli daban-daban."

12- Debula, from Kenya,Sashen Swahili na BBC

"Manufar ta kwalliyar atamfa, musamman ta al'adar Swahili. Za ka tarar da 'Kanga' a duk inda ka je. Ana dinka shi da wani tsari na kwalliyar mai zanen gida-gida aka maimaita a jikin yadin. Daga kasa kuma ana yin rubutu na karin magana."

13- Vera, daga Ghana,Editar, sashin BBC Focus on Africa

Hakkin mallakar hoto

"Manufar sa nuna asali da basira. Kwalliyar Afrika tana nuna asalina da kuma matsayina. Ko da ban kure adaka ba, zan fito daban. Na fi jin nutsuwa a cikin tufafin gargajiya. Sai ka ji kamar a gida ka ke, musamman idan kana Turai inda yawanci suturun nasara ake sanyawa. Kayan Afrika sai ta fitar da kai daban, ta nuno ka a matsayin dan asalin Afrika."

14- Ann da Nomsa da kuma Leila, wakilan BBC a Afrika ta Kudu

Hakkin mallakar hoto

"Al'adar yau da kullum ne da kuma ake samu a shaguna. Bashi da wata ma'ana a al'adance, amma sakar da atamfofin suna da kaloli da ke daukan ido."

15- Nora Fakim, daga Morocco,'Yar jarida mai aikin kai a BBC.

"Kwalliyar al'adun Afrika a gani na shi ne kwalliyar kaloli da tsare-tsre daban-daban. Nahiyar Afrika tana da fadi, kuma tana tattare da kabilu da yare da al'adun kala-kala. Wasu kwalliyar Afrika da ake gani yawanci basu nuna asalin al'adar Afrika. Yanzu haka ina sanye da tufafinKaftani na kasar Morocco inda ita kanta kasar tana da al'adun daban-daban, saboda haka akwai kaftani kala-kala daga wasu kasashe daban-daban. Saboda haka ko kaftanin Morocco aka dauka ma kadai ma ba zai wadatar ba."

16- Tulanana, daga Tanzania,'Yar jarida kuma mai hada fina-finai

Hakkin mallakar hoto

"Yadin 'Kitenge' yana da kalolin saka daban-daban, wanda matan Tanzania ke ado dashi. Ana samun sa da yadi shida har zuwa 12, inda ake dinka shi duk yadda mutum yake so. Kwanan nan ma an maida kwalliyar ta zamani, kamar wanna dinki ta 'peplum topwich' da nake sanye da shi yanzu."