Mutane 50 sun rasu a China

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Fashewar wasu abubuwa a China

Shugabannin China sun ce za a yi duk abin da ya kamata domin taimakawa wadanda fashewar wani abu ya shafa kusa da wasu masana'antu da ke tashar jirgin ruwa a garin Tianjin.

Lamarin ya janyo mutuwar akalla mutane 50 a yayinda wasu daruruwa suka jikkata.

Abubuwan sun fashe ne a wani gidan ajiyar kayan sinadarai da kuma iskar gas, inda ya rusa gidaje ya kuma kona motoci da dama.

Asibitocin Tianjin na kokarin bai wa wadanda abin ya shafa kulawa, yayinda masu aikin kashe gobara suma suna kokarin kashe wutar.

Shugaba Xi Jinping, ya ce dole ne a yi binciken musababbin fashewar abubuwan.