"Kiristoci ba sa taya Musulmai yaki da BH"

Image caption Cocin ANglican na duniya

Wani babban shugaban kiristoci a cocin Anglican na duniya, ya ce ya kamata shugabannin kiristocin Najeriya su karfafa aiki tare da Musulmai don magance barazanar da mayakan kungiyar Boko Haram ke yi ga kasar.

Archbishop Josiah Idowu-Fearon, wanda ke da mazauni a yankin arewacin Najeriya, shi ne sabon Sakatare Janar na mabiya Anglican, wacce ke da mambobi da yawan su ya kai kimanin miliyan 85 a duniya baki daya.

A hira da ya yi da BBC, ya ce wasu Kiristoci a Najeriya sun yi ta zagon kasa ga yunkurin da ya ke yi na tattaunawa tsakanin kiristoci da Musulmai, bisa fargabar cewa za'a mayar da Najeriya kasar Musulunci.

Ya ce "Mun gargadi shugabannin kungiyar kiristocin Najeriya CAN cewa ya kamata mu saurari shugabannin Musulmai saboda ba sa goyon bayan Boko Haram, amma suka ce sam-sam bakin su daya ne."

A watan Aprilu ne dai mabiya Cocin Najeriya na Anglican suka fitar da wata sanarwa, inda suka nesanta cocin ga nadin Archbishop Idowu-Fearon, saboda adawar da yake yi ga tsarin nan na sanya aikata luwadi a matsayin babban laifi.