Zafi ya hallaka mutane 61 a Masar

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mutane suna kunna fanka domin samun saukin zafi

Ma'aikatar lafiya a Masar ta ce matsanancin zafi ya janyo mutuwar mutane 61 a cikin kwanaki uku.

Lamarin ya yi kamari ne bayan da zafin ya kai ma'aunin selshiyos 47 (47C).

Kafar yada labarai ta gwamnati ya ce mutane 40 ne suka rasu a ranakun Lahadi da Litinin a yayinda 21 suka mutu a ranar Talata.

A halin yanzu akwai wasu mutane fiye da 581 da aka kwantar da su asibiti saboda gajiya tibis.

Yawancin wadanda suka rasu tsofaffi ne.