Indiya ta bukaci Nestle ya biya diyya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Taliyar Maggi noodles ta kamfanin Nestle

Gwamnatin Indiya ta bukaci kamfanin taliya na Nestle da ya biya diyyar dala miliyan 140, bayan wani gwaji da aka yi a kan taliyar ya gano cewar an samu dalma da yawa a cikin ta.

Wani jami'in gwamnati ya ce an shigar da karar ne a gaban babbar kotun da ke shari'a kan masu saye da sayarwa na kasar, tana mai zargin Nestle da rashin kyautatawa a harkar kasuwancinsa.

Tuni dai kamfanin na Nestle ya janye taliyar daga kasuwa a watan Yuni, amma ya kafe a kan cewar taliyar ba za ta cutar ba.

Nestle ya ce ba a gaya masa batun shigar da karar ba a hukumance.