Jirgi mai saukar angulu ya fadi a Lagos

Image caption Hadarin jirgin sama da aka taba yi a Lagos a shekarun baya

Wani jirgi mai saukar angulu ya fadi a Lagos, babbar cibiyar kasuwancin Nigeria.

Bayanai sun ce, mutane uku sun rasu sannan wasu ukun suka samu raunuka sakamakon hadarin.

Rahotanni sun ce jirgin helikoptan ya fadi ne a yankin Oworonsoki da ke bayan gidan basaraken gargajiya na Legas watau Oba na Lagos.

Hukumar agajin gaggawa NEMA ta tabbatar da afkuwar lamarin ga kafofin yada labarai a Lagos.

Tuni aka soma aikin ceto a wurin da jirgin ya fadi.