An tare motar fasinja a kusa da Barkin Ladi

Hakkin mallakar hoto Nigeria Police website
Image caption Sufeto Janar na 'yan sanda, Solomon Arase

Rahotanni daga jihar Filato a Nigeria na cewa wasu matasa sun tare hanya a yankin Barkin Ladi inda suka kona wata motar safa mai dauke da fasinjoji da ke wucewa a kusa da kauyen Bisichi.

Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Laraba, yayin da zaman dar-dar ke karuwa a yankin na Barkin Ladi sabo da yadda ake yawan samun riciki mai nasaba da kabilanci da addini.

Wani mazaunin kauyen Bisichi, ya shaidawa BBC cewa ga alama motar mallakin kamfanin motocin sufiri na jihar Adamawa ce, da ake kira Adamawa Sunshine, kuma kawo yanzu gawar direban motar ce kadai aka iya ganowa, yayin da fasinjojin ba a san makomarsu ba.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ta Filato, DSP Abuh Emmanuel, ya tabbatar da kona motar ta fasinja mai wucewa a yankin Bisichi, amma ya ce bai yi karin bayani ba a kan ko mutanen da ke cikin motar sun tsira ko kuma ba su tsira ba.

Rahotanni dai na cewa ana ci gaba da zaman zullumi a yankin na Bisichi, inda mazauna yankin ke cewa suna jin karar harbe-harben bindiga daga kewayensu kodayake dai 'yan bindigar basu shiga kauyen ba.