An cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Syria

Yarjejeniyar tsagaita wuta Hakkin mallakar hoto
Image caption Nan bada jima wa ba yarjejeniyar zata fara aiki

An cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta sa'o'i 48 tsakanin mayakan 'yan tawaye a Syria da kuma dakarun gwamnati a wasu garuruwa uku.

Nan bada jimawa ba yarjejeniyar za ta fara aiki.

An cimma yarjejeniyar ce domin bayar da damar aikewa da kayan abinci da magunguna zuwa yankin Zabadani da ke kusa da iyakar Labanon, inda 'yan tawayen ke da karfi da kuma kauyuka biyu da ke hannun sojojin Syria.

Kungiyar kare hakkin bil'adama a kasar Syria ta ce an cimma yarjejeniyar ce tsakanin Ahrar Al-Sham daga bangaren 'yan tawayen da kuma kungiyar Hezbollah da Iran a madadin dakarun gwamnati.