Turkiya ta soki Majalisar Dinkin Duniya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Firaiministan Turkiyya, Ahmed Davutoglu

Firai Ministan Turkiyya Ahmet Davutoglu, ya soki lamirin kasashe biyar masu kujerar din-din-din a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya bisa gazawa wajen fitar da wata matsaya domin kawo karshe tashin hankali a kasar Syria.

Kazalika Mista Davutoglu ya yi kira ga kasashen duniya da su kawo wa Syria dauki wajen ganin an kawo karshen rikicin da yaki ci yaki cinyewa a tsawon shekaru hudu.

Ya kuma musanta zargin da ake yi wa kasar tasa na marawa kungiyar IS baya da sauran kungiyoyi masu kaifin kishin Islama.

Ahmet Davutoglu, ya shaida cewa kasarsa za ta ci gaba da matsa lamba har sai ta samar da yanki na tudun mun-tsira a arewacin Syria, domin kare fararen hula wadanda hare-haren kungiyar IS da na gwamnatin Syria suka tilastawa tserewa.

Kididdiga daga Majalisar Dinkin Duniya ta nuna cewa sama da 'yan gudun hijira miliyan daya da dubu dari takwas ne ke neman mafaka a Turkiya.