Bukatar bayanan masu amfani da twitter ta ninka biyu

Image caption Masu amfani da shafin Twitter

Wani rahoton bukatar bayanan masu amfani da shafin twitter a Birtaniya ta wuce ninki biyu a shekarar 2015.

Shafin twitter ya ce hukumomin Birtaniya da kuma 'yan sandan kasar sun mika bukatu 299 a tsakanin watanni Janairu da Yuli ta neman bayanan wasu masu amfani da shafin abinda ya karu da 116 a watanni shida baya.

Hakan yasa hukumomin tsaro na Birtaniya suka kasance wadanda suka fi bukatar bayanai a kasashen kungiyar tarayyar turai.

Shafin na Twitter ya kuma ce ya amince da kashi 52 cikin 100 na bukatar neman bayanai wanda za a yi amfani da su wajen gane masu amfani da twitter.

Rabon shafin da ya fitar da rahoton ainihin yadda shafin ke tafiyar da harkokin sa ba tare da kunbiya-kunbiya ba tun a shekarar 2012.

Shafin na sada zumunta da muhawara ya ce bukatar neman bayanai daga wurinsa ta karu da kaso 52 cikin 100, karuwar da bata taba samu ba tsakanin rahoto da rahoto da ta fitar.

Shafin ya kuma ce Amurka ita ce tafi yawan bukata sai Japan sannan Turkiyya, amma Birtaniya itace tafi kowacce kasa bukata a gaba daya.

Twitter ya ce ya samu bukatar cire bayanai guda tara daga shafukan masu amfani da shi daga hukumomin Birtaniya da kuma 'yan sandan kasar .

Sai dai shafin yace abubuwan da ake bukatar a cire din sun danganci na bata suna ne ko kuma na wasu abubuwa da aka haramta sawa, amma kuma duk da hakan shafin yace ya yi watsi da duk bukatu taran.