An sauke babban jami'in MDD da ke Bangui

Hakkin mallakar hoto
Image caption Ana zargin sojoji da tafka ta'asa a Bangui

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon, ya ce ya sauke babban jami'in dakarun majalisar da ke aikin wanzar da zaman a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya daga kan mukaminsa a kan zargin da ake yi wa dakarun na yin lalata da kananan yara.

Mr Ban ya ce jami'in diplomasiyyar dan kasar Senegal, Babacar Gaye, zai sauka daga aiki a matsayinsa na jagoran rundunar kiyaye zaman lafiya a kasar.

Ban ya kara da cewa ya yi bakin ciki, kana ya yi matukar jin kunya da ya samu rahotannin yin lalata da kananan yaran.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International, ta zargi sojojin da ke aiki da rundunar wanzar da zaman lafiyar da yi wa wata yarin mai shekaru sha biyu fyade, da kuma kashe wani yaro tare da mahaifinsa a Bangui, babban birnin kasar, a farkon watan da muke ciki.

Da ma dai ana gudanar da bincike a kan yadda dakarun wanzar da zaman lafiya a kasar ta Janhuriyar Afirka ta tsakiya suka tafiyar da batun zarge-zargen da aka yi wa dakarun sojin Faransa a kan yin lalata da wasu yaran a bara.