Amurka ta yi tir da harin Damboa

Hakkin mallakar hoto Nigeria government
Image caption A baya-bayan nan ma shugaba Buhari ya gana da shugaba Obama don duba yadda za a magance matsalar tsaro

Amurka ta yi Allah-wadai da harin da aka kai wata kasuwa ta kayan wayoyi da ke kusa da Damboa a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.

Harin wanda aka kai a ranar Talata, ya yi sanadiyar mutuwar fiye da mutane 28 , yayin da wasu fiye da 78 suka jikkata.

A wata sanarwa da ofishin jakadancin Amurkan a Abuja ya fitar, ta ce Amurka za ta kara kaimi wajen ganin ta taimakawa Najeriya wajen murkushe kungiyar Boko Haram.

Ta kuma sha alwashin tallafawa wadanda hare-haren Boko Haram ya rutsa da su.

Har yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin kai harin, amma lamarin ya faru ne a wajen da kungiyar Boko Haram suka kai hare-hare a baya-bayan nan.

Tun a karshen watan Mayu da shugaba Muhammadu Buhari ya dare kan mulki, mutane kusan 800 sun rasu sakamakon hare-haren da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka kai.