Za mu cika umarnin Buhari — Sojoji

Hakkin mallakar hoto NIGERIA GOVT
Image caption Masu sharhi na ganin cewar wannan umurni na da matukar wuya ga manyan hafsoshin tsaron Nigeria

Babban hafsan sojin Najeriya ya ce za su zage damtse domin ganin cewa sun cika umarnin da shugaba Muhammadu buhari ya basu na kawar da kungiyar Boko Haram a cikin watanni uku.

Janar Abayomi Gabriel Olonisakin ya yi wannan furucin ne jim kadan bayan rantsar da shi da sauran manyan hafsoshin uku da shugaban ya yi ranar Alhamis.

A nan ne dai Shugaba Buhari ya ba su umarnin na su kawo karshen 'yan kungiyar Boko Haram a cikin watanni uku.

Ya ce lokaci yayi da za a kawo karshen Boko Haram wacce ta hallaka dubban mutane a cikin fiye da shekaru shida.

"Dole ne ku zage damtse, kuma mu ci gaba da aiki da sauran masu ruwa da tsaki domin kawo karshen masu tayar da kayar baya a cikin watanni uku," in ji Buhari.

Ya kara da cewar, "Ya zama wajibi ku kare fararen hula da kuma mutunta hakkin abokan hammaya."

Manyan Hafsohin sojin sun hada da Major-General Abayomi Gabriel Olonishakin da Major-General T.Y. Buratai da Rear Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas da kuma Air Vice Marshal Sadique Abubakar.

Tun da aka rantsar da Buhari a matsayin shugaban Nigeria a karshen watan Mayu, kungiyar Boko Haram ta hallaka mutane kusan 900.

A karshen watan Yuli ne rundunar hadin gwiwa kan yaki da Boko Haram mai dakaru 8,700 ta soma aiki.

Rundunar ta kunshi sojoji daga Nigeria da Niger da Kamaru da Chadi da kuma jamhuriyar Benin.