Za a fara gina tituna masu chajin motoci a Birtaniya

Image caption Titunan dai za su rinka guntsar haske sannan daga bisani su chaja motocin

A kasar Birtaniya, masu motocin hawa za su fara chajin ababan hawan nasu yayin da suke kan tuki, idan har shirin gwamnati na hakan ya samu nasara.

Hukuma mai alhakin gudanar da tsarin a kasar ta sanar da shirin gwajin fasahar chajin motocin wanda take shirin kakkafawa a kan titunan kasar.

Tsarin dai zai yi amfani da wata fasaha samfirin mayen-karfe ne wadda idan mota ta hau kai to kai tsaye chajin zai shige ta.

Za a binne wayoyi wadanda da suke zuko haske sannan daga bisani su mayar da hasken zuwa wutar lantarki wanda kuma zai chaja abun hawa.

Bisa wannan tsarin ababan hawan dai za su rinka tsaya wa na wani dan lokaci a kan titi domin guntsar hasken da zai chaja su.

Tuni dai an gudanar da binciken yiwuwar tsarin kuma a halin yanzu ana matakin tallata kwangilar aikin ga kamfanoni.

Sai dai wani kwararre ya nuna shakkunsa kan cewa ko kwalliya za ta biya kudin sabulu dangane da tsarin.

Kasar Korea ta kudu ce dai ta fara yin gwajin tsarin na chajin motoci akan titi, a shekarar 2013.

Image caption Motocin di za su tsaya ne a kan titunan na wani dan lokaci domin su samu chajin

Ko a shekarar 2014 ma sai da kamfanin Milton Keynes ya fara irin wannan tsarin wanda wani faranti da aka daddasa akan tituna yake samar da hasken wutar da yake chaja ababan hawan.