Wasa kwakwalwa: Shin za ka dace da kasuwanci ?

Shin ka na da kwazon soma wata harkar kasuwanci, sannan abin ya bunkasa har kamfanin ya ci riba? Galibinmu na tunanin soma wata harkar kasuwanci domin mu zama masu cin gashin kanmu.

Amma dai a kowacce harkar kasuwanci, ba a rasa 'yar matsala. In kanada minti biyu, duba irin damar da ka ke da ita a harkar kasuwanci.

Ba ruwanmu: Wannan wasa kwakwalwar ba zai tabbatar da ko mutum zai shiga kasuwanci da kafar dama ba ko kuma a'a. Hasashe ne ta yin la'akari da wasu bincike da masana suka yi.

Ta yaya aka shirya wasa kwakwalwar? Kasuwanci dadadden abu ne, amma kuma samun nasara a kasuwanci abu ne da ake ci gaba da bincike a kai. Kafin mu shirya wannan wasa kwakwalwar sai da muka yi nazari a kan wasu daga cikin binciken da masana suka yi sannan muka yi aiki tare da Brian Morgan, shehin malami a fannin kasuwanci a jami'ar Cardiff.

Daga Gerry Fletcher, Robert McKenzie, Ransome Mpini, Will Smale, Nzar Tofiq da kuma John Walton.