'Yan majalisar Girka na muhawara kan ceton kasar

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ginin Majalisar dokokin Girka

'Yan majalisar Girka sun shafe dare suna tafka mahawara akan amincewa ko akasin haka da sharuddan da kasashen turai suka gindaya wa kasar kafin a ba ta kunshin ceton kasar a karo na uku.

Ministan Kudin kasar Euclid Tsakalotos ya yi gargadin cewa idan har 'yan majalisar basu amince da sharuddan ba a cikin 'yan sa'oi masu zuwa, to taron da ministocin kudin kasashen da ke amfandi da kudin bai daya na yuro za suyi nan gaba kadan ba zai samar da bukatar kasar ta Girka ba.

Firaiministan kasar, Alexis Tsipras ya ce yana da karfin gwiwar cewa zai samu goyon bayan 'yan majalisar wajen amincewa da sharadin ceton wanda ya hada da karin haraji da rage kashe kudaden kasar.

Idan dai har 'yan majalisar suka amince da sanya wadannan sharuddan to Girkar za ta samu damar karbar bashin kudi na Yuro biliyan 85.

Kafin fara muhawarar dai, 'yan majalisar sun kwashe tsawon daren Juma'ar nan suna zazzafar tattaunawa kan batun.

Sai dai kuma babbar matsalar da firaiminista, Alexis Tsipras yake fuskanta kan amincewa da wadannan sharudda ita ce barazanar da yake samu daga kusoshin jam'iyyarsa ta Syrizia.