Guinea-Bissau: Shugaban kasa ya kori firaiminista

Hakkin mallakar hoto
Image caption Jose Mario Vaz, shugaban Guinea-Bissau

Shugaban kasar Guinea-Bissau, Jose Mario Vaz ya rushe bangaren gwamnatin da firaiministan kasar, Domingos Pereira yake jagoranta sakamakon zaman tankiyar dake tsakanin shugabannin biyu, a 'yan makonnin da suka gabata.

Shugabannin biyu dai sun kasa cimma wata matsaya dangane da batutuwan da suka shafi nada mukamai da sarrafa kudaden tallafi daga masu tallafawa kasar da kuma yarje wa tsohon babban hafsan sojin kasar, Zamoura Induta, ya dawo kasar.

Da yake yi wa 'yan kasar jawabi ta kafafen yada labarai a daren Laraba, Mario Vaz ya tabbatar da cewa alaka tsakaninsa da firaiministan ta yi tsami sosai.

Yanzu haka dai kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya ya yi kira ga dukkannin bangarorin biyu da su koma fagen tattaunawa da juna domin magance banbance-banbancen.

Kasar Guinea-Bissau ta ta yi fama da juyin mulki iri daban-daban, kafin ta dawo kan turbar demokradiyya a shekarar 2014.