Wata Kotu a Indiya ta bai wa Nestle gaskiya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Taliyar Maggie noodles a wani shago a Indiya

Wata kotu a Indiya ta ba wa kamfanin Nestle na duniya gaskiya a hukuncin da ta yanke a kan hana sayar da sananniyar taliyar Maggi Noodle.

An dage wa kamfanin hanin da aka yi masa na tsawon makonni shida har zuwa lokacin da aka yi sababbin gwaji a kan taliyar.

A cikin watan Yuni ne aka umurci kamfanin Nestle da ya janye taliyar Maggie Noodles daga kasuwar Indiya bayan da da gwaje-gwaje da aka yi a kan taliyar a wasu jihohin kasar suka nuna cewar tana dauke da sinadarin dalma dayawa.

An yanke wannan hukunci ne kwana daya bayan gwamnatin Indiya ta ce zata shigar da kara a kan Kamfanin na Nestle inda za ta nemi kamfinin ta biyata kusan dala miliyan dari.