An tsamo karin gawawwaki a Lagos

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jirgin ya fada ne a cikin ruwan Lagos

Masu aikin ceto sun tsamo karin gawawwaki biyu daga cikin ruwa na mutanen da suka mutu sakamakon hadarin jirgin sama mai saukar angulu a Lagos.

A yanzu dai adadin wadanda suka rasu sun kai shida, bayan da jirgin helikopta din ya fadi a ranar Laraba.

Kakakin hukumar agaji ta Nema a Lagos, Ibrahim Farinloye ya shaida wa manema labarai cewa wadanda suka rasu din galibinsu 'yan Nigeria ne.

Wasu mutane shida da lamarin ya rutsa da su kuma suna jinya a asibiti, kuma kawo yanzu ba a san abin da ya haddasa faduwar jirgin helikopta din ba.

Jirgin na dauke ne da mutane 12 wadanda bayanai suka ce sun taso ne daga wajen aiko hako danyen mai a cikin teku.