'Sauraron kida na rage radadin ciwo'

Image caption Tuni wasu marasa lafiya suka soma jin kida a gadon asibiti

Masu ilimin kimiyya sun ce sauraron kida kafin mara lafiya ya shiga aikin tiyata da lokacin aikin har ma kuma bayan an gama, zai taimaka wurin rage radadin ciwo.

Wani sabon bincike da aka yi a jami'an Queen Mary na London, ya nuna alamun sa'a, duk da cewa mara lafiya yana cikin nauyin bacci.

Masu binciken sun ce kida na taimakawa saboda ban da zafin fata, an fi jin zafin ciwo ne idan an sa wa rai hakan.

Dr Abdullahi Shehu, kwararren Likitan kwakwalwa ne a sabitin Jami'ar Coventry a nan Ingila ya shaidawa BBC cewa baya ga waka abin da mutun yake son ji zai iya rage masa radadin ciwo

"Sauraron karatun Kuri'ani ga masu son haka, shi ma zai iya rage radadin ciwo," in ji Shehu.

Yanzu sun bukaci asibitoci da su karfafa marasa lafiya da za a yi wa aikin tiyata, su zo asibiti da jerin wakokin da suke son ji.

Amma kuma wani binciken da aka yi a baya ya nuna cewa, sauraron kida lokacin tiyata na raba hankulin ma'aikatan asibiti.