NNPC zai rage yawan kashe kudi

Image caption Kamfanin mai na Najeriya, NNPC

Kamfanin mai na NNPC ya yi wa manyan maaikatansa kimanin talatin da takwas ritaya da nufin rage yawan kashe kudi ta yadda zai zamo ingantacen Kamfani.

A bangare guda kuma, kamfanin ya nada Mele Kyari a matsayin sabon shugaban reshensa da ke kula da sayar da danyen mai.

Haka kuma an nada Mr Ahmadu Sambo, a matsayin mai kula da ayyukan rijiyoyin mai na NNPC yayinda aka nada Mr Dafe Sejebor a matsayin mai kula da zuba jarin kamfanin na NNPC.

A cewar kamfanin, yayi hakan ne tare da amincewar shugaba Muhammadu buhari.

NNPC na samun kusan rabi ko miliyan daya na gangar mai a ko wacce rana wanda yake kasaftawa matatun mai na Najeriya ganga 445,000 a ko wacce rana.