Mutane 51 sun mutu a Bagadaza

Wata babbar mota mai dauke da bam da ya fashe a Iraqi ta kashe mutane 51 kuma mutane sama da 70 suka jikkata a Bagadaza babban birnin kasar.

Jami'ai sun ce bam din ya fashe ne a cikin kasuwar kayan lambu da ke gundumar mabiya shia a arewa maso gabashin birnin.

Kungiyar IS mai fafutukar kafa daular muslinci ta ce ita ta kai harin.

Kungiyar tana yawan kai wa 'yan Shia wadanda suke kallonsu a matsayin kafirai.