'Yan sanda za su binciki aike sakonnin batsa ta waya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wayar iPhone dai tana da fasahar aika sako ta Airdrop

'Yan sand suna bincike kan wani sabon laifi da ya kunno kai wato na aika wa mutane hotunan batsa a wayarsu, a Birtaniya.

Wannan binciken dai ya biyo bayan hotunan batsa da aka aike wa wata mace ta wayarta a lokacin da take kan hanyarta ta zuwa wurin aiki.

Matar dai ta ga hotunan na batsa har guda biyu na azzakarin wani mutum da ba ta san ko wanene shi ba.

An kuma aike da hotunan ne ta fasahar aika wa juna sakonni na Airdrop na kamfanin Apple.

A na amfani da fasahar Airdrop ne dai wajen aike sakonni ga mutanen da suke da wayar iPhone.

Lorraine Crighton-Smith mai shekaru 34 ta ce al'amarin ya ci mutuncinta na kasancewarta mace kuma ta je ofishin 'yan sanda don kai kara.

Shugabar 'yan sandar ta yankin ta ce wannan sabon laifi ne da ba rundunarta ba ta taba fuskanta ba saboda haka ta yi kira ga mutane da ka da su yi kasa a gwiwa wajen sanar da 'yan sanda irin haka idan ya afku.

Ms Crighton-Smith wadda ta kasance a cikin jirgin kasa a kudancin London, ta shaida wa BBC cewa " ina kunna fasahar karbar sako domin na sha amfani da shi a baya wajen turawa wani mai amfani da wayar iPhone sakonni, kwatsam sai na ga hoton azzakari ya bayyana a wayata al'amarin da ya yi matukar razana ni."

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mutane sun fara yin amfani da fasahar wajen aika hotunan batsa

Ta kara da cewa " daga nan sai na yi watsi da hotunan saboda rashin dacewarsu".