Samsung ya kirkiri sabbin wayoyi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wayar salula samfurin Samsung

Kamfanin Samsung ya sanar da kirkirar wasu sabbin wayoyin komai da ruwanka guda biyu wato Galaxy S6 da Galaxy Note 5.

Dukkan wayoyin girman fuskar su ya kai tsawon inchi 5.7, kuma za a fara sayar da su a cikin shekarar da muke ciki kafin a fara sayar da wadanda aka fitar kafin su.

An dai kaddamar da wayoyin ne bayan raguwar ribar da kamfanin ya ke samu a jere har sau biyar.

Masu sharhi sun ce farin jinin da wayoyin da ake kerawa a China da kuma yadda kamfanin Apple yanzu ya koma kera manyan wayoyin sa samfurin Iphone sun dakushe kasuwar Samsung.

Sai dai kuma har yanzu kamfanin na Samsung shi ne a gaba wajen samar da wayoyi a kasashen duniya.

Samsung ya kuma sanar da cewa zai kaddamar da wani tsari inda za a rinka amfani da wayarsa wajen cinikayya wadda ake kira Samsung Pay, za a kaddamar da wannan tsari ne a ranar 20 ga watan Augusta a Koriya ta kudu.

Kamfanin mallakar kasar Koriya ta kudu, ya ce zai fadada yin amfani da wannan tsari zuwa Amurka a ranar 28 ga watan gobe, sannan tsarin zai kuma isa Birtaniya da Spaniya anan gaba.

Kazalika Samsung ya ce sabuwar wayar kirar Galaxy Note 5 ta na da irin biron nan da ake rubutu dashi.

A wani sauyin tsarin kasuwanci da kamfanin na Samsung ya bullo da shi, shi ne ba zai samar da irin wadannan sabbin wayoyi da ya fitar ba a nahiyar turai.