'Yan Majalisar Girka sun amince da tallafi a karo na uku

Hakkin mallakar hoto
Image caption Firayi Ministan Girka Alexis Tsipras

Majalissar dokokin Girka ta amince a baiwa wa kasar kunshin tallafi a karo na uku. Majalissar ta amince da hakan ne 'yan sa'oi kafin Ministocin kudi na kasashen turai za su amince su bayar da tallafin Euro biliyan 85.

Bayan sun shafe dare suna tafka muhawara a garin Athens, Firayi minstan Girkan Alexis Tsipras ya bukaci 'yan mjalissar su amince da sharuddan tallafin.

Firayi ministan ya kara da cewar kawo wani tsarin na daban zai sa Girka ta cigaba da kasancewa cikin matsalar tattalin arziki har abada.

Rahotanni a cewar Mr Tsipras zai nemi 'yan majalisar su kada kuri'ar karfafawa gwamnatinsa baya a mako mai zuwa wanda hakan zai sa yiwuwar zabe nan kusa.