Zamfara: Gada ta kashe mutum daya

Rahotanni daga jihar Zamfara a Najeriya na cewa akalla mutum daya ya rasa ransa bayan da gadar Danmarke da ke kan hanyar Sokoto zuwa Gusau da ta rufta a farkon wannan mako ta kara ruftawa inda motoci biyu suka fada cikin ramin.

A ranar Litinin aka sake bude hanyar bayan da hukumomi suka yi wa gadar gyara na wucin gadi sakamakon karyewar da ta yi a farkon makon.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Gadar dan marke ta rufta a makon da ya gabata

Bangaren da aka yi wa gyaran ya kuma rugujewa ne sakomakon ruwa da aka yi kamar da bakin kwarya a daren ranar Alhamis.