Zawahiri ya yi mubaya'a ga shugaban Taliban

Image caption al-zawahiri ne ya maye gurbin Osama Bin Laden

Shugaban kungiyar Al-Ka'ida, Ayman al-Zawahiri ya yi mubaya'a ga sabon shugaban kungiyar Taliban, Mullah Akhtar Mansour.

Ya bayyana haka ne a sakon muryarsa da aka wallafa a intanet.

Wannan shi ne sako na farko da al-Zawahiri ya aika, tun a watan Satumbar bara.

Zawahiri kuma ya mika ta'aziyarsa bisa rasuwar tsohon shugaban Taliban, Mullah Omar.

Masu sharhi na kallon mubaya'ar a matsayin wani mataki na ci gaba da kawance tsakanin kungiyar Al-Ka'ida da kuma Taliban ganin cewar a yanzu akwai wata kungiyar masu ikirarin jihadi watau IS.