An yi jana`izar Mataimakin Gwamnan Borno

Marigayi Alhaji Zannah Mustapha Hakkin mallakar hoto Borno Govt Facebook
Image caption Mataimakin Gwamnan Jihar Borno, Alhaji Zannah Mustapha

An yi jana`izar mataimakin Gwamnan jihar Borno, Alhaji Zannah Umar Mustapha a Maiduguri, babban birnin jihar

Gwamnatin Jihar ce ta sanar da rasuwar Mataimakin Gwamnan mai shekara 49 da haihuwa.

Mataimakin Gwamnan ya rasu ne yau da asuba a Yola, babban birnin jihar Adamawa, inda ya je wakiltar Gwamnan Borno a wajen bikin yaye daliban jami'ar fasaha ta Modibbo Adama.

Tuni dai gwamnan jihar Bornon, Alhaji Kashim Shettima ya bayyana alhini dangane da wannan rashi, yana adu'ar Allah ya gafarta masa.