An nada shugaban tace fina-finai

Gwamnan jihar Kano Alh Abdullahi umar Ganduje
Image caption Gwamnatin jihar Kano na son kawo gyara a hukumar tace fina-finan jihar.

A karon farko gwamnatin Kano ta nada dan fim a matsayin shugaban hukumar tace fina finai ta jihar.

Wanda aka nada Isma'ila na Abba wanda aka fi sani da Afakallah shine shugaban kungiyar masu shirya fina finai ta Arewa AFMAN reshen jihar Kano.

Sabon shugaban tsohon mai shiryawa ne da bada ummarni da kuma fitowa a cikin fina finan Hausa

Wannan shine karo na farko da gwammnatin jihar ta nada wani dan fim a matsayin shugaban hukumar mai sa ido akan shiryawa da kuma bayar da izinin sayar da finafinan a Kano da kuma wasu jihohin arewacin kasar.

A shekarun baya dai hukumar ta yi kaurin suna wajen kamawa da daure 'yan fim da marubuta da mawaka da kuma 'yan kasuwa a bisa karya dokokin hukumar wanda ake ganin sun yi tsauri.

Cikin wadanda hukumar ta daure a baya sun hada da Hamisu Iyan Tama da marigayi Rabbilu Musa dan Ibro da Sani Danja da kuma Adam A. Zango.

'Yan fim a jihar sun dade suna fafutukar ganin an nada wani daga cikinsu kan wannan mukami hakan bai samu sai a yanzu.

Ana zargin hukumar da mayar da hankali wajen kamawa da daure 'yan fim fiye da bunkasa fasaha da kuma shirin fim a jihar.