Japan na nadamar yakin duniya na biyu

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Basaraken gargajiya Akihito na Japan

Basaraken gargajiya Akihito a Japan ya bayyana rashin jin dadin sa dangane da abin da ya faru a yakin duniya na biyu.

Akihito ya ce abin da ya faru lokacin yakin ba za a kara maimata tashi ba.

Dubban mutane ne suka ziyarci wani kebabben wajen ibada domin tunawa ga mutanen da suka rasa rayukansu a lokacin yakin duniyar.

An gudanar da bukuwan ne domin tunawa da zagayowa shekaru sabain da kawo karshen yakin duniya na biyu a Kasashen Japan da Koriya ta kudu.

Firaministan Japan Shinzo Abe ya ce kasarsa ta yi nadama da wahalhulan da ta janyowa alummar yankin.

Mika wuyan da Japan din tayi a lokacin yakin dai shi ya ba wa kasar Korea ta kudu samun 'yanci daga Japan bayan kwashe shekaru 35 a karkashinta.