Muna sa Ido a gwammnatin APC in ji PDP

pdp
Image caption PDP yanzu ita ce jam'iyyar adawa a Najeriya bayan ta shafe shekaru 16 tana mulki

A Najeriya wasu 'yan jamiyyar PDP sun ce zasu ci gaba da sa ido don ganin ko jam'iyyar APC mai mulkin kasar za ta iya cika alkawuran data yi wa talakawa.

A hirarsu da wakilin BBC Alh Adamu Maina Waziri tsohon minista a ma'aikatar harkokin 'yan sanda ta kasar kuma dan takarar gwamna a jihar Yobe a zaben da ya gabata, ya yi watsi da tururuwar da wasu 'yan PDPn ke yi zuwa APC mai mulki.

Ya kara da cewa suna kallon takun jam'iyyar APCn mai mulkin.

Jam'iyyar PDP dai ta shafe shekaru 16 tana mulki a kasar bayan ta sha kaye a hannun jam'iyyar APC a zaben da ya gabata a yanzu ta koma jam'iyyar adawa.