Tattaunawa a Sudan ta Kudu ta ci tura

Shugaba Salva Kiir da Riek Machar Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sudan ta Kudu dai ta dade ta na fuskantar tashe-tashen hankula, tun bayan da ta balle daga kasar Sudan.

Yiwuwar tattaunawar sulhu da za ta kawo karshen yakin basasar da ake yia Sudan ta kudu ta ci tura, bayan da aka sanar da cewa shugaban Sudan ta Kudun ba zai halarci zaman sulhun da 'yan tawaye ba.

Mai magana da yawun shugaba Salva Kiir yace ba zai yi tattaki har zuwa Adidis Ababa babban birnin kasar Habasha ba a karshen wannan mako.

Sai dai yace gwamnatin Sudan ta Kudun ba ta na nufin nuna rashin goyon baya ga tattauna da 'yan tawayen ba, wadda tsohon mataimakinsa Riek Machar ke jagoranta.

Masu shiga tsakani dai sun sanya ranar litinin mai zuwa a matsayin ranar da za kammala tattaunawa dan kawo karshen yakin da ake yi tsakanin bangarorin biyu, wanda ya yi sanadiyyar raba mutane kusan miliyan biyu da muhallinsu yayin da wasu daruruwa suka rasa rayukan su.