Jita-jitar Apple zai kera motoci ta tabbata

Kayayyakin kamfanin Apple Hakkin mallakar hoto Pasu Au Yeung FlickrCC
Image caption An san Apple da natsuwa wajen kirkiro abin da yake mai nagarta da inganci

Jita-jitar cewa kamfanin Apple zai fara kera motoci dai wani abin alfahari ne ga dimbim magoya bayan kamfanin wadanda suke fatan samun wani sabon abu daga kamfanin.

A yanzu dai gaskiya ta yi halin ta bayan da jaridar The Guardian ta samu kwafin daya daga cikin wasikun da aka yi tsakanin wani ijiniya kamfanin Apple Frank Fearon da kuma wasu jami'ai na kamfanin dake gwajin motoci GoMentum Station.

Wasikar na bayani ne akan bukatar da kamfanin Apple ya gabatar don nema lokaci da kuma sarari don yin gwajin motar da aka kera.

A baya dai an yi ta rade radin cewa kamfanin na Apple yana daukar hayar kwararru daga kamfanin da ke kera mota mai amfani da wutar lantarki irinsu Tesla da kuma masu yin baturan mota.

Kuma an ce suna aikin kera wata mota a shekaru da dama a asirce.

An kuma san Apple da tsayawa ya natsu ya kirkiro abin da yake mai nagarta da inganci ba wai kawai ya kirkiri abin da kawai za a ce shi ma ya bullo da nasa ba.

A matsayinsa na kamfani Apple da alamu ba ya damuwa ya ce wai sai ya zama na daya a kasuwa, burinsa kawai shi ne ya yi abin da za a saya da daraja.