Komla: BBC ta karrama Kucingira

Image caption Nancy Kacungira

BBC ta karrama 'yar jaridan nan 'yan kasar Yuganda, Nancy Kacungira da lamabar yabonta ta farko da ta fara bayarwa domin tunawa da tsohon mai gabatar da shirye-shiryenta Komla Dumor.

Komla Dumor dai ya mutu ne a shekarar da ta gabata yana da shekaru 41.

Ita dai Ms Kacungira ta zamanto zakara ce cikin kusan mutane dari biyu da suka shiga cikin gasar bayan fafatawa mai zafi.

Ms Kacungira ta bayyana farin cikinta, kuma ta ce manufarta ita ta sauya tunanin mutane game da nahiyar Afirka wadda aka dade ganinta a matsayin koma-baya, sakamakon haka ne ta samu basirar labarin da ya kai ta ga nasara.

Ms Kacungira wacce ta ke aiki a gidan talabijin na KTN da ke Kenya, zata yi watanni uku a BBC a London.