Boko Haram ta kai hari a kusa da Damasak

Image caption Rikicin Boko Haram ya raba dubun dubatan mutane da muhallansu

Rahotani daga jihar Borno sun ce 'yan Boko Haram sun kai hari a garin Awunari da ke kusa da Damasak.

Bayanai sun ce an kai harin a ranar Litinin da safe, lamarin da ya janyo hasarar rayuka da kuma wani mutum daya da ya jikkata.

Wadanda suka tsallake rijiya da baya sun ce wadanda suka kai harin sun je kauyen ne a kan babura.

Yankin na Damasak na cikin wuraren da ke karkashin ikon dakarun hadin gwiwa na kasashen Chadi da kuma Nijar da suka janye a baya-bayan nan.

Lamarin na zuwa ne kwana guda bayan da shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau ya fitar da sako na sauti inda ya musanta zargin cewar an kashe shi.