Ebola ba ta sake bulla a Saliyo ba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta ce babu wanda ya kamu da cutar Ebola a makon da ya gabata, tun farkon bullar ta.

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce a karon farko tun bullar cutar Ebola a Saliyo, babu wanda ya kamu da cutar a makon da ya gabata a kasar.

Sai dai duk da haka, hukumomi a kasar, suna gargadin mutane da su yi taka-tsan-tsan don kaucewa ci gaba da yaduwar cutar.

Za dai a iya bayyana cewa an kawo karshen cutar ne idan aka shafe makwanni shidda babu wanda ya kamu da cutar a kasashe ukun da ta bulla.

Kasashen su ne Liberia, da Saliyo da Guinea.

Babu alamun cutar a Liberiya tun watan da ya gabata, sai dai an samu rahoton cutar ta shafi mutane uku a kasar Guinea.